Jarumai mata da suka rasu suna da karancin shekaru, da kuma dalilin mutuwarsu | KANNYWOOD | fadila |

Sdílet
Vložit
  • čas přidán 27. 09. 2020
  • Babu shakka mutuwa dole ce, tunda Allah ne ya tabbatar da cewa kowacce rai sai ta dandana zafinta.
    Masana'antar fina-finan Hausa wacce aka fi sani da Kannywood, ta dandana rashe-rashe da dama. Daga ciki kuwa akwai na 'yan matan masana'antar wadanda suka shahara.
    Ga wasu daga cikin 'yan matan masana'antar da suka rasa rayukansu da kananan shekarunsu:
    1. Fadila Muhammad: Fitacciyar jarumar masana'antar fina-finan hausa wacce ta yi sharafi daga shekarar 2011 zuwa 2014,
    Tana daya daga cikin jarumai masu matukar salo da farin jini a masana'antar.
    Matashiyar jarumar tana da wani irin salo na bayyana a wasan kwaikwayo, wanda ke saka zukatan masu kallo cikin nishadi.
    Tauraruwarta ta fara haskawa tun bayan da ta fito a fina-finai masu suna Hubbi da Basaja. Babu shakka wadannan fina-finan sun saka sunanta ya dauku ga ma'abota kallon fina-finan Hausa.
    jarumar ta rasu a daren Juma'a, 28 ga watan Augustan 2020 da misalin karfe 11 na dare a cikin motar mahaifinta yayin da yake kokarin kaita asibiti.
    Kafin rasuwar Tata dama jarumar na fama da ciwon zuciya. Bayan kwana daya kafin mutuwarta ta ciwon ya taso mata inda Aka mikata sibiti a ranar ta samu sauki kuma aka mayar da ita gida. Ciwon ya sake tashi, wanda bai sake lafawa sai dai tafiya da ranta da yayi.
    Jarumar mai shekaru 27 a duniya an yi mata sallar jana'izarta da misalin karfe 8:30 na safiyar Asabar a gidan iyayenta da ka fagge Close, Unguwar Dosa da ke Kaduna.

    2. Maryam Aliyu: Marigayiya Maryam na daga cikin 'yan matan masana'antar fina-finan hausa masu matukar farin jini a lokacin da take raye.
    Ta bayyana a fitattun fina-finai masu suna Sarki Goma, Rugunstumi da Attajirai. Ta rasu ne yayin da take nakuda za ta haihu a cikin watan Afirilun 2011.
    Ta rasu tana da shekaru 25 a duniya, kuma ta bar mijinta Musbahu M. Ahmed, wanda jarumi a masana'antar.
    3. Safiyya Ahmed:
    Babu shakka za a ci gaba da tunawa da ita a kan gudumawar da ta bada wajen ficen masana'antar. Wasu daga cikin fitattun fina-finan jarumar sun hada da Ruduntsumi da Gobe ma Rana ce. Ta rasu tana da shekaru 27.
    Marigayiyar jaruma Safiyya ta rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiyar da tayi a garin Kano a 2010. Hazikar jarumar na cikin sharafinta yayin da mutuwa ta dauketa.
    4. Balaraba Muhammad: Balaraba jaruma ce da ta yi farin jini a masana'antar fina-finai sakamakon hazaka da iya gogewa a wasan kwaikwayo da tayi.
    Allah ya karba rayuwar jaruma Balaraba Muhammad a ranar 13 ga watan Maris na shekarar 2002.
    Ta rasu sakamakon mummunan hatsarin da suka yi a kan titin Zaria zuwa Kano.
    Marigayiyar ta rasu yayin da ake kan hanyar kai ta dakin mijinta bayan daura musu aure da aka yi da jarumi Shu'aibu Lawan, wanda aka fi sani da Kumurci.
    Za a ci gaba da tunawa da jarumar mai shekaru 18, sakamakon rawar da ta taka a fina-finan Furuci, Dawayye da Tasiri.
    Allah ya jikansu da gafara, ya kyautata zuwan tamu. Ameen
    #gaskiya24_tv #gaskiya24 #mubarakeey_tv #dj_ab #adam_a_zango #zool_wsh #Bushkiddo #Arewa24 #kwana_casa_in #hausatop #sabon_comedy #baba_buhari #waka #karatu #wakokin #gidan_badamasi #kannywood #kannywoodcelebrities #Arewa24 #hausa #siyasa #koyon #kashe #ayatullahi_tage #mazajene #chizo_1_Germany #aliartwork #zazafa #gomna #pantami #yadda_ake #hausa_song #sheikh #ali_nuhu #maryam_yahaya #sani_danja #ali_jita #umar_m_sharif #hamisu_breaker #tuna_baya #iskanci #garzali #nomiis_gee #morell #dadin_kowa #malam #rarara #hausa_song_2020 #ado_gwanja #hausa_comedy #hadiza_gabon #jaruman #zafafa10 #kundin_kannywood #nazifi_asnanic #nigeria #arewa #boko_haram #sojoji #abubakar_shekau #izzar_so
  • Zábava

Komentáře • 64