Rayuwar Dattijuwa Mai Sana'ar Ga-Ruwa A Kano

Sdílet
Vložit
  • čas přidán 9. 09. 2024
  • Hajiya Aisha Isiya, dattijuwa ce da ta shafe fiye da shekara daya tana sana’ar ga-ruwa domin kula da mijinta da ’ya’yanta a unguwar Sauna da ke karamar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano.
    Ganin rufin asirin da ta fara samu ya sanya sauran matan unguwar suka rungumi sana’ar, inda suke gogayya da maza wajen daukar ruwa jarka biyu-biyu a lokaci guda, su kuma shigar har cikin gida su juye wa mai saye.
    Sai dai Hajiya Aisha ta ce babban burinta a yanzu shi ne ta samu wata sana’ar da za ta fidda ta daga kangin talauci, domin ta samu ta gyara gidansu da ke yoyo a lokacin damina, ta kuma dinga biya wa ’ya’yanta kudin makaranta saboda a daina koro su gida.

Komentáře • 6